ABNA24 : Kungiyar ta Palasdinawa ta kaddamar da daftarin kuduri ga kungiyar kasashen larabawan akan matakin na Hadaddiyar Daular Larabawa akan HKI, sai dai kasashen yankin tekun pasha da kuma Masar, Jordan, Sudan da Morroco, sun ki amincewa da shi, amma da Hadaddiyar Daular Larabawa ta gabatar da nata kuduri, sai wadannan kasashen dai su ka amince da shi.
Tashar talabijin din ‘almayadeen’ ta bayar da labarin cewa; Gwamnatocin Somalia da ta Hadi Mansur na Yemen ne kadai su ka ki yarda, yayin da kasashen Iraki, Lebanon, Aljeria, da Tunisia su ka zama ‘yanba-ruwanmu akan daftarin kudurin Hadaddiyar Daular Larabawa.
Sakataren Kungiyar ‘yanto Palasdinu Sa’ib Uraiqat ne ya yi barazanar cewa za su fice daga kungiyar ta larabawa,idan har ta amince da shirin na Hadaddiyar Daular Larabawa.
342/